Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Yadda Takura A Wajen Aiki Ke Ta'azzara Rayuwar Ma'aikaci
•
Aminiya
A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba.
Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadda za a warware damuwa a irin wannan yanayi.