Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
'Amfani Da Tsaffin Takardun Naira Zai Iya Jefa Mutum A Matsala'
•
Aminiya
Mutane da dama sun shaida cewa takardar Nairar Najeriya na saurin lalacewa.
Wasu na ganin masu liki a wajen bukukuwa da yadda ake kasuwancin sabbin kudi na taka rawa. Toh amma me ya kamata a yi, me kuma doka tace kan kudin da suka tsufa suka lalace.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba halin da mutum zai iya jefa kansa idan har aka same shi da wulakanta takardun Naira da yadda za a bada gudummuwa wajen inganta kudin.