Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Abin Da Ke Sa Fararen Hula Su Raina Sojoji
•
Aminiya
Mu’amalar farar hula da sojoji a Najeriya ta mutuntuwa ce wadda zarar aka hangi soja a cikin gari jiki har karkarwa yake.
Sai dai a ‘yan kwanakin nan a iya cewa yadda labarai ke yawan fita game da yadda fararen hula ke yin tsaurin ido wajen takalar sojoji da fada yana karuwa.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa fararen hula ke kokarin daga hannunsu kan jami’an tsaro musamman na soji.