Daga Laraba

Dalilin Da Maza Ba Su Son Likita Namiji Ya Duba Matansu

Muslim Muhammad Yusuf

A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci.

Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su.

Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.