Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
‘Na Yi Nadamar Ajiye Aiki Saboda Tsohon Mijina’
•
Muslim Muhammad Yusuf
Yayin da wasu mazan suke kyale matansu su yi aiki, wasu kan yi kememe su ki bari nasu matan su yi.
Shin barin matar aure ta yi aiki ne ya fi alheri ko hana ta? Wadanne dalilai kowanensu ke da su?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a cikin wannan lamari.