Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau
•
Muslim Muhammad Yusuf
Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah.
A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.