Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro
•
Muslim Muhammad Yusuf
Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.