Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Matakan Kauce Wa Hadarin Ambaliyar Ruwa
•
Muslim Muhammad Yusuf
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa.
A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine.
Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.