Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
•
Muslim Muhammad Yusuf, Suleiman Hassan Ibrahim
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya.
Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali.
Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.