Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda
Daga Laraba
Daga Laraba
Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda
Aug 14, 2024
Muslim Muhammad Yusuf da Suleiman Hassan Jos

A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna.

A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya.

To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi?

Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da juna.