Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci
Daga Laraba
More Info
Daga Laraba
Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci
Jan 26, 2022
Aminiya

Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21.

Alakar mutane da harkokin sadarwa ta zamani ta sa kusan harkokin kasuwanci sun tasamma komawa intanet, a wasu lokutan kuma ana amfani da wayar tarho ne wurin assasa harkokin kasuwanci da kuma tabbatar da su. 

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi waiwaye kan irin halin ni-’yasun da harkokin kasuwancin suka shiga a sakamakon rufe layukan sadarwa a kwanakin baya a Jihar Katsina.