Alamu sun fara nuna yadda sauyin yanayi zai shafi daminar bana, bayan hasashen hukumomin Najeriya suka yi kan ruwan sama da kuma katsewarsa a farkon daminar.
Ana ciki haka sai ga wata guguwa mai karfin gaske da ta shafi jihohin Adamawa da Katsina a makon jiya.
Mun tattauna da Hukumar lura da yanayi ta Najeriya da kuma masanin kimiyyar noma domin jin yadda za a tunkari wadannan kalubalenen.