Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kara Naira Dubu Ashirin Da Biyar kan albashin kananan ma’aikatan Najeriya A jawabinsa na ranar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kan kasar nan.
Ta wadanne bangarori wannan kari zai shafi rayuwar ku?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu, ya ji ta bakin masana, ya kuma binciko shin bayan watanni shida sun cika sai kuma mene ne abin yi na gaba daga fadar shugaban Najeriya.