Najeriya a Yau

Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Marasa Inganci Nan Take

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Ana yawan cin karo da kayan abinci ko na sha da basu da inganci, kuma ga dukkan alamu sun cika sharuddan sahihanci a ido.

 Hukumomi na yawan kama  darurwan kwalaben kayan sha da ci na jabu ne amma kuma ga su dauke da lambar dake nuna sahihancin su.  Akwai masu kirkirar kayan jabu da dama domin shigar da su kasuwa.

Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda za ku gane kayyakin da ba su da inganci a tashin farko.