Sana’o’i na samun cikas da koma baya a wasu sassan Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki. A yan kwanakin nan ana yawan kokawa da yadda wutar lantarki ke ƙara tabarbarewa.
Masu sharhi na ganin da ace za a samu ingattaciyar wutar lantarki a Najeriya, to da cigaban da za a samu ya wice misali.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda rashin lantarki ke durkusar da kasuwanci a kasar.