Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe
•
Muslim Muhammad Yusuf
Batun cire sarakun da aka faro ta kamar wasa ga shi ta tabbata.
Sarki Sanusi shi ne sarkin da ya sake dawowa bayan tube sarakuna biyar na jihar, lamarin da za a iya cewa wasu sun yi hasashen hakan tun da fari.
Shin mene ne mataki na gaba da ya rage wa sarakunan? Ya alaka za ta kasance tsakanin wadanna gidajen sarautar. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.