Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cututtuka Da Damina
•
Muslim Muhammad Yusuf
A yankuna da dama an fara samun ruwan sama, duk da cewa damina ba ta yi karfi ba a wasu wuraren.
Bayanai sun nuna cewa a irin wannan lokaci Kwalara ko amai da gudawa da Maleriya da Thypoid da dai sauransu na cikin cututtukan da ke saurin yaduwa.
Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan wasu daga cikin waɗannan cututtuka da matakan kauce musu.