Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Dawo Da Tsohon Taken Ƙasa Zai Mayar Da Najeriya Baya
•
Muslim Muhammad Yusuf
Dawo da tsohon taken Najeriya da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shan yabo da suka.
Mutane da dama dai na cewa a yanzu talakan Najeriya ba abin da yake bukata ba ke nan.
Shirin Najeriya a Yau zai duba alfanun dawo da taken da muhimmancinsa a mizanin bukatun ’yan Najeriya.