Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Me Manoma Suka Shirya Wa Daminar Bana?
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
A yayin da damina ta fara kankama a wasu sassan Najeriya, fatan manoma shi ne samun yabanya mai kyau.
Akwai matakan da masana ke ganin ya kamata manoma su dauka duk a lokacin da ruwa ya fara sauka domin kauce wa lalacewar amfanin gona.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan matakan da suka kamata manoma za su dauka a wannan yanayi.