Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Tamowa Ke Nema Ta Gagari Kundila A Arewa
•
Muslim Muhammad Yusuf da Ummu Salmah Ibrahim
Kiraye-kiraye na karuwa game da matakin da ya kamata a dauka don dakile matsalar karancin abinci mai gina jiki wato tamowa a jikin kanan yara
Kungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta ce an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya.
Shirin Najeriya a Yau zai duba matakan da za ya kamata a dauka don kare kai daga kamuwa da tamowa.