Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
'Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata'
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
Gwamnatocin Kananan Hukumomi sun koka cewa za a dora musu nauyi idan har aka amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Sai dai ma’aikatansu na ganin ba su dalilin fadin hakan, ganin yadda suka samu ninkin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur.
Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin yadda za a warware wannan takaddama.