Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Mutum Zai Iya Cinye Naman Layyarsa Shi Kadai?
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
A lokacin Bikin Babbar Sallah da mutane kan yi layya, ana sa ran wanda bai yi ba ma ya samu ya ci nama.
Amma wasu masu karamin karfi kan bayyana yadda makwabtansu da suka yi layya sukan shige da namansu gida su yi tuwo-na-mai-na.
Shirin Najeriya a Yau zai duba halalcin yin hakan a Musulunce.