Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Ko Kalaman Kwankwaso Sun Kaɗa Hantar APC Ne?
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
Wasu kalaman da jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya furta yana zargin Gwamnatin Tarayya suna ci gaba da tayar da kura.
Fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC a matakin kasa da jihar Kano sun yi kakkausan suka da kiran a yi maza-maza a kama shi.
Shin me ya girgiza Jam’iyyar ta APC game da wadannan kalamai? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wannan turka-turka.