Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Kimar Sarakunan Gargajiya A Idon Al’ummar Arewa
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim da Sulaiman Hassan
A baya-bayan nan ana samun muhawara, wani lokaci ma zazzafa, a kan kimar masarautun gargajiya.
Shin yaya al’umma ke kallon sarakunan gargajiya a halin yanzu?
Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan kimar masu rike da masautun gargajiya a wannan zamani.