Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hanyoyin Magance Kuncin Da ‘Yan Najeriya Suke Ciki
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim, Sulaiman Ibrahim
Ana ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu.
Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi.
Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘yan kasa.