Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abin Da Dokar Ta-Baci Kan Man Fetur Ke Nufi
•
Muslim Muhammad Yusuf
Ana ta musayar ra’ayin bayan da Kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar.
Mutane na neman amsar shin me hakan ke nufi, da muhawarar ko hakan abu mai yiwuwa ne?
Shirin Najeriya a Yau nzai tattauna kan abin da dokar ta baci kan man fetur ke nufi.