Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda
Jul 11, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Sulaiman Hassan

Send us a text

A wannan makon babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman ya samu ni’imar cika shekara 100 a duniya.

Malamai da mabiya da al’umma sun jinjina yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Addini.

Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan gudummuwar da Shehin Malamin ya bayar a cikin shekara fiye da 70 da ya yi yana karantar da Al-Kur’ani.