Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Wane Sauyi 'Yancin Cin Gashin Kai Zai Kawo A Kananan Hukumomi?
•
Muslim Muhammad Yusuf, Sulaiman Hassan
Hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi ya jefa su cikin farin ciki a fadin Najeriya.
Sai dai yanzu abin da ake son ganin ya faru shi ne yaushe wannan tsari zai yi tasiri kuma me ya rage ga kananan hukumomi.
Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin bakin kan abin da hukuncin ya kunsa da mataki na gaba ga kanana hukumomi.