Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
Jul 16, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Sulaiman Hassan Ibrahim

Send us a text

A yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi.

Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci.

Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da Ashura da muhimmancin shi ga rayuwar Musulmai.