Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
Najeriya a Yau
Najeriya a Yau
Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
Sep 10, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Daga cikin manyan hakkokin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dorawa shugabanni, shine kirkirar dabarun samarwa Yan kasa saukin tsadar Rayuwa da tabbatar da kasancewar su cikin walwala.

Sai dai, a baya-bayan nan, Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa irin dabarun da shugabanninin ke amfani dasu wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Shirin Najeriya a Yau ya tattauna ne, kan irin dabarun da suka kamata shugabanninin Najeriya suyi amfani dasu, wajen magance matsalolin da ake ciki.