Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hakikanin Abin Da Ya Faru A Owo, Jihar Ondo
•
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
A Ranar Lahadin da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka kai farmaki kan wasu masu ibada, a wata cocin Katolika da ke kusa da gidan sarkin Owo wanda kuma garin gwamna Oluwarotimi Akeredolu ne na jihar Ondo. Sun kashe masu ibada da dama suka kuma jikata wasu.
Shirin Najeriya a yau ya dubi yadda Al'amarin ya faru.