Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe
Najeriya a Yau
Najeriya a Yau
Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe
Oct 07, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Matasa da dama a Najeriya ne suka yi sake-reshe-kama-ganye saboda hangen Dala.

Saboda tunanin zai samu kudi masu yawa ta hanyar kudin kirifto na Hamster, John Adams ya yi murabus daga aikinsa, daga karshe ya tashi ba tsuntsu ba tarko – ma’ana, babau aikin babu kudin.

Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne a kan halin da wadannan matasa suka tsinci kan su ciki bayan mining din Hamster.