Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya
Najeriya a Yau
Najeriya a Yau
Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya
Dec 23, 2024
Idris Bature

Send us a text

Lokacin da Victoria Faith, wata baiwar Allah mai shekara 27 da haihuwa, ta je coci a Gundumar Maitama da ke birnin Abuja, cike take da kyakkyawan fatan samo abincin da za ta yi bikin Kirsimeti da shi.

Amma a maimakon haka da kyar ta tsira da ranta, ta yi “sa’a” da ta farka a gadon asibiti, bayan da aka tattake ta a turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai saurari yadda Victoria ta ji, sannan ya yi nazari a kana bin da yake haddasa turmutsutsu a tasakanin ’yan Najeriya, da ma hanyoyin hana shi aukuwa.