Tun bayan da jihar kano ta fitar da rahoton ware zunzurutun kudi har naira biliyan biyu da rabi don auratar da marasa aure a jihar ne dai batun ke ta shan suka daga bangarori daban daban a fadin Najeriya.
Wasu na ganin jihar na da wasu bukatun da suka fi auratar da alumma muhimmanci da ya kamata ace gwamnatin ta mayar da hankali a kai.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi nazari ne kan dalilan da suka sa jihar Kano ta ware Naira Biliyan Biyu da rabi don aurar da ‘yan mata da zawarawa.