Tun bayan bayyana kafa Gwamnatin Bibiya ko kuma Shadow government a turance da wata kungiya karkashin jamiyyar APC a jihar kano tace zata yi ne ne dai alumma da dama keta jefa ayar tambaya kan halascin wannan gwamnati.
Kungiyar dai ta bayyana cewa zata kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata.
Sai dai wannan sanarwa na cigaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halascin kafa wannan gwamnatin Bibiya a jihar Kano.