A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zulumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar.
Wadannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da ikirarin Gwamnati na cewa an yi nasarar nakasa kungiyar.
Ko mene ne dalilin sake farfadowar kungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci?
Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.